Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 10:14-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba.

15. Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan 'ya'yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.

16. Fir'auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

17. Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.”

18. Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna, ya tafi ya roƙi Ubangiji.

19. Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.

20. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuwa ya ƙi sakin Isra'ilawa.

21. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.”

Karanta cikakken babi Fit 10