Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 9:3-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.

4. Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato mushe.

5. Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan'uwansa.

6. “Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.

7. Amma ku, ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”

8. Allah kuwa ya ce wa Nuhu da 'ya'yansa.

9. “Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku,

10. da kowane mai rai da yake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya.

11. Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

12. Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa,

Karanta cikakken babi Far 9