Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 9:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku.

3. Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.

4. Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato mushe.

5. Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan'uwansa.

6. “Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.

7. Amma ku, ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”

8. Allah kuwa ya ce wa Nuhu da 'ya'yansa.

Karanta cikakken babi Far 9