Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 9:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah kuwa ya sa wa Nuhu da 'ya'yansa albarka, ya ce musu, “Ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku cika duniya.

2. Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku.

3. Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.

Karanta cikakken babi Far 9