Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 6:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9. Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.

10. Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.

11. Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina.

12. Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

13. Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.

14. Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro.

Karanta cikakken babi Far 6