Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 6:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.

5. Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.

6. Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai.

7. Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”

8. Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9. Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.

10. Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.

11. Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina.

Karanta cikakken babi Far 6