Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 6:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi 'ya'ya mata,

2. sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.

3. Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”

4. A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.

5. Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.

6. Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai.

7. Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”

8. Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9. Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.

10. Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.

11. Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina.

12. Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

13. Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.

14. Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro.

Karanta cikakken babi Far 6