Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 5:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.

19. Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza.

20. Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.

21. Sa'ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela.

22. Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi 'ya'ya mata da maza.

23. Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar.

24. Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.

25. Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek.

26. Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.

27. Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.

28. Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,

29. ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.”

30. Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza.

31. Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba'in da bakwai, ya rasu.

Karanta cikakken babi Far 5