Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 5:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah.

2. Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su.

3. Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu.

4. Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza.

5. Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.

6. Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh.

7. Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza.

8. Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.

9. Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan.

10. Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

11. Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.

12. Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel.

13. Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

14. Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.

15. Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared.

Karanta cikakken babi Far 5