Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 48:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sa'ad da nake zuwa daga Mesofotamiya, sai Rahila ta rasu a hannuna a ƙasar Kan'ana a kan hanya, ga shi kuwa, da sauran tazara kafin a kai Efrata. Na kuwa binne ta a Efrata,” wato Baitalami.

8. Sa'ad da Isra'ila ya ga 'ya'yan Yusufu, maza, ya ce, “Su wane ne waɗannan?”

9. Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “'Ya'yana ne maza waɗanda Allah ya ba ni a nan.”Sai ya ce, “Kawo su gare ni, ina roƙonka, domin in sa musu albarka.”

10. Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.

11. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na 'ya'yanka.”

12. Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra'ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.

Karanta cikakken babi Far 48