Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 48:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sa'ad da Yusufu ya ga mahaifinsa ya ɗora hannun damansa a bisa kan Ifraimu, ransa bai so ba, ya ɗauke hannun mahaifinsa, domin ya kawar da shi daga kan Ifraimu zuwa kan Manassa.

18. Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “Ba haka ba ne baba, gama wannan ne ɗan fari. Sa hannunka na dama a bisa kansa.”

19. Amma mahaifinsa ya ƙi, ya ce, “Na sani, ɗana, na sani, shi ma zai zama al'umma, zai ƙasaita, duk da haka ƙanensa zai fi shi ƙasaita, zuriyarsa kuwa za ta zama taron al'ummai.”

20. Ya sa musu albarka a wannan rana, yana cewa,“Ta gare ku Isra'ila za su sa albarkada cewa,‘Allah ya maishe ku kamar Ifraimuda Manassa.’ ”Da haka ya sa Ifraimu gaba da Manassa.

21. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka.

22. Ni ne nake ba ka Shekem, kashi ɗaya fiye da 'yan'uwanka, wanda na ƙwace da takobina da bakana daga hannun Amoriyawa.”

Karanta cikakken babi Far 48