Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 47:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir'auna, ya ce, “Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan'ana, yanzu suna ƙasar Goshen.”

2. Daga cikin 'yan'uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir'auna.

3. Sai Fir'auna ya ce wa 'yan'uwan nan nasa, “Mece ce sana'arku?”Suka amsa wa Fir'auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.”

4. Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”

5. Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka.

6. Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”

7. Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka.

8. Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”

9. Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”

10. Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna.

11. Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta.

12. Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.

Karanta cikakken babi Far 47