Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 45:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa.

8. Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir'auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.

9. “Ku gaggauta, ku hau zuwa wurin mahaifina ku ce masa, ‘Ga abin da Yusufu ɗanka ya ce, “Allah ya maishe ni shugaban Masar duka, ka gangaro wurina kada ka yi wata wata.

10. Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da 'ya'yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi.

11. A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.’ ”

Karanta cikakken babi Far 45