Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 45:25-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan'ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu.

26. Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.

27. Amma sa'ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa'ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo.

28. Isra'ila ya ce, “I, ya isa, ɗana Yusufu yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”

Karanta cikakken babi Far 45