Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 44:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa,

2. ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa.

3. Gari na wayewa aka sallami mutanen da jakunansu.

4. Tun ba su riga suka yi nisa da garin ba, Yusufu ya ce wa mai hidimar gidansa, “Tashi, ka bi mutanen, in ka iske su ka ce musu,

5. ‘Don me kuka rama alheri da mugunta? Don me kuka sace mini finjalina na azurfa? Da shi ne mai gidana yake sha, da shi ne kuma yake yin istihara. Kun yi kuskure da kuka yi haka.’ ”

6. Lokacin da ya iske su sai ya yi musu waɗannan maganganu.

7. Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan!

8. Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan'ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?

9. Daga cikinmu barorinka, duk wanda aka sami abin a wurinsa, bari ya mutu, mu kuwa mu zama bayinka, ranka ya daɗe.”

10. Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.”

11. Nan da nan kowa ya saukar da taikinsa ƙasa, kowa kuwa ya buɗe taikinsa.

12. Ya bincika, ya fara daga babba zuwa ƙarami, sai aka iske finjalin a cikin taikin Biliyaminu.

13. Suka kyakkece rigunansu, kowannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin.

Karanta cikakken babi Far 44