Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 41:48-57 Littafi Mai Tsarki (HAU)

48. sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.

49. Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.

50. Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu 'ya'ya biyu maza, waɗanda Asenat 'yar Fotifera, firist na On ta haifa masa.

51. Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”

52. Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”

53. Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika,

54. aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci.

55. Sa'ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir'auna kuka domin abinci, sai Fir'auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.”

56. Domin haka sa'ad da yunwar ta bazu ko'ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.

57. Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.

Karanta cikakken babi Far 41