Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 41:41-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.”

42. Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,

43. ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar.

44. Har yanzu dai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir'auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.”

45. Fir'auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat 'yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.

46. Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.

47. A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske,

48. sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.

49. Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.

50. Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu 'ya'ya biyu maza, waɗanda Asenat 'yar Fotifera, firist na On ta haifa masa.

51. Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”

52. Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”

Karanta cikakken babi Far 41