Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 38:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan.

5. Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.

6. Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar.

7. Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi.

8. Sa'an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan'uwanka, ka yi mata wajibin ɗan'uwan miji, ka samar wa ɗan'uwanka zuriya.”

9. Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan'uwansa zuriya.

10. Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi.

11. Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.

12. A kwana a tashi, ga matar Yahuza, 'yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta'aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba'adullame.

13. Sa'ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,”

14. sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.

15. Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta.

Karanta cikakken babi Far 38