Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 38:22-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ”

23. Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.”

24. Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.”Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”

25. Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”

26. Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.

27. Sa'ad da lokaci ya yi da za ta haihu, ashe, cikin tagwaye ne.

28. Da tana cikin naƙuda, sai hannun wani ya fara fitowa, ungozoma kuwa ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, tana cewa, “Wannan shi ya fara fitowa.”

29. Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan'uwansa ya fito, sai ta ce, “A'a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa.

30. Daga baya ɗan'uwansa ya fito da jan zare a hannunsa, aka kuwa sa masa suna Zera.

Karanta cikakken babi Far 38