Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 38:17-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.”Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”

18. Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?”Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki.

19. Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba.

20. Sa'ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba'adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba.

21. Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?”Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.”

22. Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ”

23. Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.”

24. Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.”Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”

25. Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”

26. Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.

Karanta cikakken babi Far 38