Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 38:14-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.

15. Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta.

16. Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce.Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?”

17. Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.”Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”

18. Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?”Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki.

19. Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba.

20. Sa'ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba'adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba.

21. Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?”Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.”

22. Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ”

Karanta cikakken babi Far 38