Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 38:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya zama fa a wannan lokaci, Yahuza ya bar 'yan'uwansa ya gangara, ya zauna wurin wani Ba'adullame mai suna Hira.

2. A can, sai Yahuza ya ga 'yar wani Bakan'ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta,

3. ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, ya kuwa raɗa masa suna Er.

4. Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan.

5. Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.

6. Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar.

7. Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi.

8. Sa'an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan'uwanka, ka yi mata wajibin ɗan'uwan miji, ka samar wa ɗan'uwanka zuriya.”

9. Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan'uwansa zuriya.

10. Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi.

Karanta cikakken babi Far 38