Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 36:23-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Waɗannan su ne 'ya'yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.

24. Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon.

25. Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana.

26. Waɗannan su ne 'ya'yan Dishon, maza, Hemdan da Eshban, da Yitran, da Keran.

27. Waɗannan su ne 'ya'yan Ezer, maza, Bilhan, da Zayawan, da Akan.

28. Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran.

29. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,

30. da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.

31. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra'ilawa.

32. Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba.

33. Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa.

Karanta cikakken babi Far 36