Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 36:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, wato Edom.

2. Isuwa ya auri matansa daga cikin Kan'aniyawa, wato Ada 'yar Elon Bahitte, da Oholibama 'yar Ana ɗan Zibeyon Bahiwiye,

3. da Basemat, 'yar Isma'ilu, 'yar'uwar Nebayot.

4. Ada ta haifa wa Isuwa, Elifaz, Basemat kuma ta haifi Reyuwel.

5. Oholibama ta haifi Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa waɗanda aka haifa masa a ƙasar Kan'ana.

6. Isuwa ya kwashi matansa, da 'ya'yansa mata da maza, da dukan jama'ar gidansa, da shanunsa, da dabbobinsa duka, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan'ana, ya kuwa tafi wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu.

7. Gama abin mallakarsu ya yi yawa har ba zai yiwu su zama tare ba, ƙasar baƙuntarsu kuwa ba ta wadace su ba saboda yawan dabbobinsu.

8. Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom.

9. Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, kakan Edomawa, a ƙasar Seyir ta tuddai.

10. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isuwa, maza, wato Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.

11. 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz.

12. Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa.

13. Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.

14. Waɗannan su ne 'ya'yan Oholibama matar Isuwa 'yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora.

Karanta cikakken babi Far 36