Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 35:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai Yakubu ya zo Luz, wato Betel, wadda take cikin Kan'ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi.

7. A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa.

8. Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.

9. Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.

10. Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra'ila.” Don haka aka kira sunansa Isra'ila.

11. Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.

12. Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.”

Karanta cikakken babi Far 35