Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 32:13-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan'uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi,

14. awakai metan da bunsurai ashirin, tumaki metan da raguna ashirin,

15. raƙuman tatsa talatin tare da 'yan taguwoyi, shanu arba'in da bijimai goma, jakai mata ashirin da jakai maza goma.

16. Waɗannan ya sa su a hannun barorinsa ƙungiya ƙungiya, ya ce wa barorinsa, “Ku yi gaba, ku ba da rata tsakanin ƙungiya da ƙungiya.”

17. Ya umarci na kan gaba, ya ce, “Sa'ad da Isuwa ɗan'uwana ya gamu da ku, ya tambaye ku cewa, ‘Ku mutanen wane ne? Ina za ku? Waɗannan da suke gabanku na wane ne?’

18. Sa'an nan sai ku ce, ‘Na Yakubu baranka ne, kyauta ce zuwa ga shugabana Isuwa, ga shi nan ma biye da mu.’ ”

19. Da haka nan ya umarci na biyu da na uku da dukan waɗanda suke korar garkunan, ya ce, “Sai ku faɗa wa Isuwa daidai haka nan.

20. Ku kuma ce, ‘Ga shi ma, Yakubu ɗan'uwanka yana biye da mu.’ ” Gama, cikin tunaninsa ya ce, “Ya yiwu in gamshe shi da kyautar da ta riga ni gaba, daga baya in ga fuskarsa, watakila ya karɓe ni.”

21. Saboda haka kyautar ta yi gaba, shi kansa kuwa a daren, ya sauka a zango.

22. A wannan dare kuwa ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da kuyanginsa biyu da 'ya'yansa goma sha ɗaya ya haye mashigin Jabbok.

23. Ya ɗauke su ya haye da su rafi, haka kuma ya yi da dukan abin da yake da shi.

24. Aka bar Yakubu shi kaɗai.Sai wani mutum ya kama shi da kokawa har wayewar gari.

25. Sa'ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi.

26. Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.”Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”

27. Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?”Ya ce, “Yakubu.”

28. Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”

29. Sa'an nan Yakubu ya tambaye shi, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.”Amma ya ce, “Don me kake tambayar sunana?” A nan mutumin ya sa masa albarka.

30. Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.”

Karanta cikakken babi Far 32