Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 28:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Saboda haka Isuwa ya tafi wurin Isma'ilu ya auro Mahalat 'yar'uwar Nebayot, 'yar Isma'ilu ɗan Ibrahim, banda matan da yake da su.

10. Yakubu ya bar Biyer-sheba ya kama hanya zuwa Haran.

11. Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci.

12. Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!

13. Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.

14. Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka.

15. Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”

16. Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.”

17. Ya tsorata, sai ya ce, “Wane irin wuri ne wannan mai banrazana haka! Ba shakka wannan wurin Allah ne, nan ne kuma ƙofar Sama.”

18. Sai Yakubu ya tashi tun da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al'amudi, ya kuwa zuba mai a kan al'amudin.

Karanta cikakken babi Far 28