Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 28:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ya tsorata, sai ya ce, “Wane irin wuri ne wannan mai banrazana haka! Ba shakka wannan wurin Allah ne, nan ne kuma ƙofar Sama.”

18. Sai Yakubu ya tashi tun da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al'amudi, ya kuwa zuba mai a kan al'amudin.

19. Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz.

20. Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa,

21. har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna,

22. wannan dutse kuwa wanda na kafa shi al'amudi zai zama wurin sujada ga Allah. Daga cikin dukan abin da ya ba ni, zan ba shi ushirinsa.”

Karanta cikakken babi Far 28