Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 25:27-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Sa'ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida.

28. Ishaku ya ƙaunaci Isuwa saboda yakan ci naman da ya farauto, amma Rifkatu ta ƙaunaci Yakubu.

29. Wata rana, sa'ad da Yakubu yake dafa fate, Isuwa ya komo daga jeji, yana jin yunwa ƙwarai.

30. Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom.

31. Yakubu ya ce, “Sai dai ko in yau za ka sayar mini da matsayinka na ɗan fari.”

32. Sai Isuwa ya ce, “Ni da nake bakin mutuwa, wane amfani matsayina na ɗan fari zai yi mini?”

33. Yakubu ya ce, “Yau sai ka rantse mini.” Sai ya rantse masa ya kuwa sayar wa Yakubu da matsayinsa na ɗan fari.

34. Sa'an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.

Karanta cikakken babi Far 25