Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 25:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura.

2. Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa.

3. Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. 'Ya'yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le'umomim.

4. 'Ya'yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka 'ya'yan Ketura ne.

5. Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi.

6. Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.

7. Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba'in da biyar.

8. Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi.

9. Ishaku da Isma'ilu 'ya'yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre,

10. wato saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa.

11. Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.

12. Waɗannan su ne zuriyar Isma'ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

Karanta cikakken babi Far 25