Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 23:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.

3. Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa,

4. “Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”

5. Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce,

6. “Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”

7. Ibrahim ya tashi ya sunkuya wa Hittiyawa, mutanen ƙasar.

8. Sai ya ce musu, “Idan kun yarda in binne matata in daina ganinta, to, ku ji ni, ku roƙar mini Efron Bahitte ɗan Zohar,

9. ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.”

10. A sa'an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce,

11. “Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama'ata na ba ka ita, ka binne matarka.”

Karanta cikakken babi Far 23