Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 23:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama'ata na ba ka ita, ka binne matarka.”

12. Ibrahim kuwa ya sunkuya a gaban jama'ar ƙasar.

13. Ya ce wa Efron, a kunnuwan jama'ar ƙasar, “In dai ka yarda, ka ji ni. Zan ba da kuɗin saurar. Ka karɓa daga gare ni don in binne matata a can.”

14. Efron ya amsa wa Ibrahim,

15. “Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.”

16. Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.

17. Don haka saurar Efron da yake cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka

18. an tabbatar wa Ibrahim, cewa mallakarsa ce a gaban Hittiyawa, a gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsu.

19. Bayan wannan, Ibrahim ya binne Saratu matarsa a kogon da yake a saurar Makfela a gabashin Mamre, wato Hebron, cikin ƙasar Kan'ana.

20. Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.

Karanta cikakken babi Far 23