Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 23:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya,

2. sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.

3. Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa,

4. “Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”

5. Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce,

6. “Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”

Karanta cikakken babi Far 23