Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 2:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu.

2. A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.

3. Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.

4. Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa'ad da aka halicce su.A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama,

5. a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar,

6. amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka.

7. Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

8. Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata.

9. Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12

Karanta cikakken babi Far 2