Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 19:24-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama,

25. ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire.

26. Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri.

27. Da sassafe kuwa sai Ibrahim ya tafi wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji,

28. ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar.

29. Amma sa'ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.

30. Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da 'ya'yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da 'ya'yansa biyu mata.

31. Sai 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Mahaifinmu ya tsufa, ba wanda zai aure mu yadda aka saba yi ko'ina a duniya.

32. Zo dai, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi, sa'an nan sai mu kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”

Karanta cikakken babi Far 19