Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 18:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima.

4. Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace,

5. ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da yake kun biyo ta wurin baranku.”Sai suka ce, “Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.”

6. Ibrahim kuwa ya gaggauta zuwa cikin alfarwa wurin Saratu, ya ce, “Ki shirya mudu uku na gari mai laushi da sauri, ki cuɗa, ki yi waina.”

7. Sai Ibrahim ya sheƙa zuwa garke, ya ɗauki maraƙi, matashi mai kyau, ya ba baransa, ya kuwa shirya shi nan da nan.

8. Ya ɗauki kindirmo da madara, da maraƙin da ya shirya, ya ajiye a gabansu, ya tsaya kusa da su a gindin itacen a sa'ad da suke ci.

9. Suka ce masa, “Ina Saratu matarka?”Ya ce, “Tana cikin alfarwa.”

10. Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne.

Karanta cikakken babi Far 18