Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 11:8-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin.

9. Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.

10. Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu.

11. Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

12. Sa'ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela.

13. Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

14. Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber,

15. Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

16. Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg,

17. Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

18. Sa'ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu.

19. Feleg ya yi shekara metan da tara bayan haihuwar Reyu, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

20. Sa'ad da Reyu ya yi shekara talatin da biyu ya haifi Serug.

21. Reyu kuwa ya yi shekara metan da bakwai bayan haihuwar Serug, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

22. Sa'ad da Serug ya yi shekara talatin ya haifi Nahor,

23. Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

24. Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera,

Karanta cikakken babi Far 11