Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 11:24-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera,

25. Nahor kuwa ya yi shekara ɗari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

26. Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.

27. Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu.

28. Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa.

29. Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya.

30. Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato ba ta da ɗa.

31. Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kalidiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can.

32. Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.

Karanta cikakken babi Far 11