Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 10:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya.

9. Shi riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji, domin haka akan ce, “Shi kamar Lamirudu ne riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji.”

10. Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke.

11. Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala,

12. da Resen wadda take tsakanin Nineba da Kala, wato babban birni.

13. Mizrayim shi ne mahaifin Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Neftuhawa,

14. da Fatrusawa, da Kasluhawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.

15. Kan'ana ya haifi Sidon ɗan farinsa, da Het,

16. shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,

17. da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa,

18. da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan'aniyawa suka yaɗu.

19. Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha.

20. Waɗannan su ne 'ya'yan Ham, bisa ga iyalansu, da harsunansu da ƙasashensu, da kabilansu.

Karanta cikakken babi Far 10