Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 10:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. 'Ya'yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana.

7. 'Ya'yan Kush kuma Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama kuwa Sheba da Dedan.

8. Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya.

9. Shi riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji, domin haka akan ce, “Shi kamar Lamirudu ne riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji.”

10. Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke.

11. Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala,

Karanta cikakken babi Far 10