Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 10:23-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. 'Ya'yan Aram kuma Uz, da Hul, da Geter, da Meshek.

24. Arfakshad ya haifi Shela, Shela ya haifi Eber.

25. An haifa wa Eber 'ya'ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan.

26. Yokatan ya haifi Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera,

27. da Adoniram, da Uzal, da Dikla,

28. da Ebal, da Abimayel, da Sheba,

29. da Ofir, da Hawila da Yobab, dukan waɗannan 'ya'yan Yokatan ne.

30. Yankin ƙasar da suka zauna shi ne ya milla tun daga Mesha, har zuwa wajen Sefar, ƙasar tudu ta gabas.

31. Waɗannan su ne 'ya'yan Shem bisa ga iyalansu, da harsunansu, da ƙasashensu, da kabilansu.

Karanta cikakken babi Far 10