Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 10:17-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa,

18. da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan'aniyawa suka yaɗu.

19. Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha.

20. Waɗannan su ne 'ya'yan Ham, bisa ga iyalansu, da harsunansu da ƙasashensu, da kabilansu.

21. An kuma haifa wa Shem, wan Yafet, 'ya'ya, shi ne kakan 'ya'yan Eber duka.

22. 'Ya'yan Shem su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram.

23. 'Ya'yan Aram kuma Uz, da Hul, da Geter, da Meshek.

24. Arfakshad ya haifi Shela, Shela ya haifi Eber.

25. An haifa wa Eber 'ya'ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan.

26. Yokatan ya haifi Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera,

Karanta cikakken babi Far 10