Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 10:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne zuriyar 'ya'yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu 'ya'ya.

2. 'Ya'yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras.

3. 'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.

4. 'Ya'yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.

5. Daga waɗannan ne mazauna a bakin gāɓa suka yaɗu bisa ga ƙasashensu, kowanne da harshensa, bisa ga iyalansu da kabilansu.

Karanta cikakken babi Far 10