Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 9:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan da aka gama waɗannan abubuwa, sai shugabanni suka zo wurina, suka ce, “Mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato su Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa, da Amoriyawa.

2. Gama sun auro wa kansu da 'ya'yansu 'yan matan mutanen nan. Yanzu tsattsarkar zuriya ta cuɗanya da mutanen ƙasashe. Shugabanni da magabata sun fi kowa laifi kan wannan rashin gaskiya.”

3. Sa'ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.

4. Sa'an nan dukan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra'ila, saboda rashin aminci na waɗanda suka komo daga zaman talala, suka taru, suka kewaye ni sa'ad da nake zaune a ruɗe, har lokacin yin sadakar yamma.

5. A lokacin sadakar yamma ɗin, sai na tashi daga yin azumi, da rigata da alkyabbata yagaggu. Na rusuna a gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Ubangiji Allahna.

6. Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.

Karanta cikakken babi Ezra 9