Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 7:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.

17. Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa ƙarfi kamar ruwa.

18. Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanƙo a kawunansu.

19. Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya ƙosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu.

20. Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su ƙazantattun abubuwa a gare su.

21. “Zan ba da su ganima ga baƙi, da kwaso ga mugayen mutanen ƙasar. Za su lalatar da su.

22. Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su ƙazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su ƙazantar da shi.

23. “Sai ka ƙera surƙa, gama ƙasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi.

24. Zan kawo al'ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu ƙarfi ta ƙare. Za a ƙazantar da masujadansu.

25. Sa'ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.

26. Masifa a kan masifa, jita-jita a kan jita-jita. Suna neman wahayi daga wurin annabi, amma doka ta lalace a wurin firist, shawara kuma ta lalace a wurin dattawa.

27. Sarki yana makoki, yarima kuma zai fid da zuciya. Hannuwan mutanen ƙasar sun shanye saboda razana. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su kamar yadda suka hukunta waɗansu. Za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Ez 7