Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 41:8-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Na ga harsashi mai faɗi kewaye da Haikalin. Tsawon harsashin gini na ɗakunan karan awo mai tsawon kamu shida ne.

9-10. Kaurin katangar waje ta ɗakunan kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan waje da na Haikali kamu ashirin ne kewaye da Haikalin.

11. Ana buɗe ƙofofin ɗakuna a wajen filin da yake tsakanin ɗakuna. Ƙofa ɗaya tana fuskantar wajen arewa, ɗaya kuma tana fuskantar wajen kudu. Faɗin filin da ya ragu kamu biyar ne.

12. Ginin da yake fuskantar farfajiyar Haikali a wajen yamma, faɗinsa kamu saba'in ne. Kaurin ginin kamu biyar ne, tsawonsa kuma kamu tasa'in ne.

13. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu ɗari. Tsawon farfajiyar, da ginin, da katangarsa, kamu ɗari.

14. Faɗin Haikalin da farfajiyar a fuskar gabas, kamu ɗari.

15-16. Ya kuma auna tsawon ginin da yake fuskantar farfajiyar da take wajen yamma da hanyar fita, kamu ɗari ne. Cikin Haikalin, da ɗaki na can ciki, da shirayi, dukansu uku suna da tagogi masu gagara badau. An manne bangon Haikalin da yake fuskantar shirayin da katako, tun daga ƙasa har zuwa tagogi. [Tagogin kuma an rufe su.]

17-18. An zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a bangon Haikali ciki da waje har zuwa kan ƙofar shiga. Zanen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu.

19. Fuska ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe. Ɗaya fuskar kamar ta sagarin zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zana dukan jikin bangon Haikalin da su.

20. Daga ƙasa zuwa ɗaurin ƙofa, an zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino.

21-22. Madogaran ƙofofin Haikalin murabba'i ne. Akwai wani abu mai kama da bagaden itace a gaban Wuri Mai Tsarki, tsayinsa kamu uku ne, tsawonsa kamu biyu ne. Kusurwoyinsa da gindinsa, da jikinsa na itace ne. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.”

23. Haikali da Wuri Mai Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe.

24. Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje.

25. A ƙofofin Haikalin an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangon Haikalin. Akwai rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin waje.

26. Akwai tagogi masu gagara badau a kowane gefen ɗakin. An kuma zāna bangon da siffar itatuwan dabino.

Karanta cikakken babi Ez 41