Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 36:26-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi.

27. Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka'idodina.

28. Za ku zauna cikin ƙasar da na ba kakanninku. Za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku.

29. Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba.

30. Zan sa 'ya'yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al'ummai.

31. Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama.

32. Ni Ubangiji Allah na ce, sai ku sani, ba saboda ku ba ne zan aikata wannan. Ku kunyata, ku gigita saboda hanyoyinku, ya mutanen Isra'ila!”’

33. Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da zan tsarkake ku daga dukan muguntarku, zan sa ku zauna cikin biranenku, ku gina rusassun wurare.

34. Ƙasar da take kufai a dā za ku kafce ta maimakon yadda take kufai a kan idon dukan masu wucewa.

35. Za su ce, ‘Wannan ƙasa wadda take kufai a dā ta zama kamar gonar Aidan, ga kuma rusassun wuraren da suka zama kufai, da rusassun birane, yanzu ana zaune a cikinsu, an kuma gina musu garu.’

36. Sa'an nan al'umman da suka ragu kewaye da ku za su sani, ni Ubangiji na sāke gina rusassun wuraren da suka zama kufai. Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”

37. Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki.

38. Kamar garken tumaki na hadaya, kamar garken tumaki a Urushalima a lokacin ƙayyadaddun idodi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Ez 36