Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 36:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Zan sa dukan mutanen Isra'ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare.

11. Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.

12. Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.

13. “Ni Ubangiji Allah na ce, da yake mutane sukan ce muku, 'Kuna cinye mutane, kuna kuma kashe 'ya'yan al'ummarku,

14. saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe 'ya'yan al'ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15. Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al'umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama'a ba, ba kuma zan ƙara sa al'ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

16. Ubangiji Kuma ya yi magana da ni, ya ce,

17. “Ɗan mutum, sa'ad da mutanen Isra'ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta.

18. Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu.

19. Na warwatsa su cikin al'ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu.

20. Amma sa'ad da suka tafi cikin al'ummai, sai suka ɓata sunana mai tsarki a duk inda suka tafi. Sai mutane suka yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan jama'ar Ubangiji ne, amma dole ne su fita daga cikin ƙasarsa.’

21. Amma na damu saboda sunana mai tsarki wanda mutanen Isra'ila suka sa aka ɓata shi a wurin al'ummai inda suka tafi.

22. “Domin haka sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ba saboda ku ba ne, ya mutanen Isra'ila, zan yi wani abu, amma saboda sunana mai tsarki wanda kuka ɓata a wurin al'ummai inda kuka tafi.

23. Zan ɗauki fansa saboda sunana mai tsarki, mai girma, wanda aka ɓata a wurin al'ummai, ku kuma kuka ɓata shi a cikinsu. Al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tabbatar da tsarkina a wurinku a kan idonsu.

Karanta cikakken babi Ez 36