Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 36:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Kai ɗan mutum, ka yi annabci a kan duwatsun Isra'ila, ka ce, ‘Ya duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji.’

2. Ubangiji Allah ya ce, da yake maƙiya suna cewa, ‘Madalla, tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu,’

3. sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane.

4. Domin haka, ku duwatsun Isra'ila, sai ku ji maganar Ubangiji Allah. Ni Ubangiji Allah, na ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, da kufai, da yasaassun birane waɗanda suka zama ganima da abin ba'a ga al'umman da suke kewaye,

5. ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al'umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.’

6. “Domin haka ka yi wa ƙasar Isra'ila annabci, ka ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al'ummai.’

7. “Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al'umman da suke kewaye da ku su ma za su sha zargi.

8. Amma ku, ya duwatsun Isra'ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanen Isra'ila, gama za su komo gida ba da jimawa ba.

9. Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka!

10. Zan sa dukan mutanen Isra'ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare.

11. Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.

12. Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.

13. “Ni Ubangiji Allah na ce, da yake mutane sukan ce muku, 'Kuna cinye mutane, kuna kuma kashe 'ya'yan al'ummarku,

14. saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe 'ya'yan al'ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15. Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al'umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama'a ba, ba kuma zan ƙara sa al'ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 36