Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 29:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Za su zama rarraunan mulki a cikin mulkoki. Ba za su ƙara ɗagawa sauran al'umma kai ba. Zan sa su zama kaɗan, har da ba za su ƙara mallakar waɗansu al'ummai ba.

16. Ba za su ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra'ila ba, gama Isra'ilawa za su tuna da laifin suka yi, suka nemi taimakon Masarawa. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”

17. A kan rana ta fari ga watan fari a shekara ta ashirin da bakwai, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

18. “Ɗan mutum, Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya sa sojojinsa su matsa wa Taya. Kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta yi kanta, amma duk da haka shi, tare da sojojinsa, bai sami hakkin wahalar da ya sha a Taya ba.”

19. Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Zan ba Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ƙasar Masar, zai kwashe dukiyarta, ya lalatar da ita, ya washe ta ganima. Za ta zama abin biyan sojojinsa.

20. Na ba shi ƙasar Masar saboda wahalar da ya sha, gama ni suka yi wa aiki. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

21. “A ranan nan zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda ya zama babban sarki, zan kuma buɗe bakinka a tsakiyarsu. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Ez 29